Hausa
Yadda talauci ke addabar mutanen karkara a Najeriya
Yadda talauci ke addabar mutanen karkara a Najeriya

Wani rahoto da kungiyar dake sanya Ido kan wanzuwar talauci da raguwarsa ta world poverty clock ta fidda ya ce akalla ‘yan Najeriya miliyan 71 ne ke rayuwa a cikin matsanancin talauci a kasar.
Faruk Mohammad Yabo ya duba mana yadda matsalar talauci ke ci wa mutanen kauye tuwo a kwarya musamman a wannan lokacin da gwamnatin kasar ta janye tallafin man fetur.