Hausa

An gurfanar da miji bisa cizon leɓen mai-ɗakin sa

Wani magidanci mai shekaru 40, Ayodeji Abayomi, a yau Alhamis a ka gurfanar da shi a wata kotun majistare da ke Iyaganku a Ibadan, jihar Oyo bisa zargin sa da cizon leɓen mai-ɗakin sa na ƙasa.

Ƴansanda ne ke tuhumar Abayomi, wanda ba a ba da adireshin gidansa ba, da laifin cin zarafi.

Dan sanda mai shigar da kara, Philip Amusan, ya shaida wa kotun cewa wanda ake ƙarar ya aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Afrilu da misalin karfe 7 na safe a unguwar Abebi, Ibadan.

Amusan ya yi zargi Abayomi da cizon leɓen matarsa na ƙasa, ya kuma ce sunan matar ​​Lilian.

Ya ce laifin ya saɓawa sashe na 335 na kundin dokokin laifuka na jihar Oyo, 2000.

Sai dai Abayomi, ya musa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Alkalin kotun, O. A. Akande, ya bada belin wanda ake ƙara a kan kudi naira dubu 50 tare da mutane biyu masu tsaya masa.

Ta kuma dage sauraron karar har sai ranar 5 ga watan Yuni.

Related Articles

Back to top button