Contact Information

Nun Street Maitama Abuja

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar Jarrbawar bawar Neco ta sanar da Sakin  Sakamakon Jarrabawar NECO 2022 a ranar 29 ga watan Satumba 2022.

Hukumar tayi Karin haske game da yadda dalibai suka sami makin jarrabawr inda tace”  adadin dalibai da suka sami Credit a yaren turanci wato Engkish sun kai 74.8%  sannan kuma ta kara da cewa dalibai kuwa da suka taka mahimmiyar rawa a bangaren lissafi sun kai 78.23%.

Ta kuma ce daliban da suka sami makin da ake bukata da suka hadar da turanci da lissafi sunkai adadin 60.74%

Sannan ta kara da cewa daliban da suka zauna jarrabawar ta wannan shekara ta 2022 sunkai 1,198,412.

Zaka iya duba sakamakon ta wannan hanyoyi:

a. Wayar Hannu

b. Computer

yadda za’a duba:

Dafarko dalibi zai kasance yana  da daya daga cikin abinda aka anbata a sama domin samun damar duba sakamakon jarrabawar daga gida sannan ya kasance inda dalibi yake akwai wadataccen network, bayan an samu dukkan wadan nan za’a shiga shafin hukumar Neco https://result.neco.gov.ng/

Sannan a tabbata an sayi Scratch card ko kuma Token a shafin hukumar ko kuma wajen ‘yan kasuwa mafi kusa.

Da zarar an shiga shafin za’aga jadawalin kamar haka:

  1. Exam Year: sai a sanya shekarar 2022
  2. Exam Type: Shima sai a shiga a Zaba
  3. Token: shine scratch card din da aka saya sai a sanyashi a wannan gurbi
  4. Registration Number: ita ce lambar jarrabawar dalibin wace hukumar jarrabawar neco ta samar ga ko wane dalibi.
  5. Sai a danna CHECK RESULT daga nan sai Sakamakon ya bayyana inda za’aiya printing nan take ko kuma a ajiyeshi.
Share:

administrator