Gwamnatin Najeriya ta ce shirin fitar da ‘yan kasar miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekara ta 2030 zai iya samuwa idan masu ruwa da tsaki suka taka rawar da ya kamata.
Kachollum Daju, sakatariyar dindindin ta ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, ta bayyana hakan a lokacin da take jawabi ga manema labarai ranar Lahadi a Abuja.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin gwamnati na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.
Misis Daju ta ce rawar da manyan jami’a za su taka a kamfanoni masu zaman kansu, ciki har da abokan huldar ci gaba ya kasance ba makawa, kuma gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an cimma burinta.
Ta ce ma’aikatu da hukumomin gwamnati (MDAs) suna aiki tukuru don ganin an aiwatar da aikin fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talauci. Ta ce ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi ta kaddamar da wani bankin bayanai, wanda aka fi sani da Labour Market Information System (LMIS) don jagorantar wadanda aka dauka aiki da kuma masu son samun aikin yi. A cewarta, tare da sabon tsarin ci gaban kasa na 2021 zuwa 2025, na tabbata kuna sane da cewa akwai bangarori da dama na iya cigaba