Contact Information

Nun Street Maitama Abuja

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Ɗalibai daga ko wanne  ɓangare na jihar kano sun gudnar da jarrabawar ta makarantar Science and Technical Kano ta shekarar 2022 tun watannin baya, inda iyaye da ɗalibai ke dakon ganin sakamakon nasu domin motsawa izuwa mataki nagaba.

Hukumar makarantar ta kammala aikin sakamakon jarrabawar inda zai zama nunanne a yanar gizo-gizo a ranar Litinin 12 September, 2022 kamar yadda muka sami sahihan cin hakan a official website ɗinta.

Yadda Ake Duba Sakamakon Science and Technical Schools Board:

  1. Abu na farko dai za’a ɗauko takardar da aka baiwa ɗalibi tun a baya wace take ɗauke da Lamabar Jarrabawar ɗalibin da kuma shekarun haihuwa, domin sai dasu ne za’a iya fidda sakamakon.
  2. Za’a shiga shafin makarantar Science and Technical Kano Board inda a nan ne za’a sanya dukkan abinda aka ambata a sama, sannan a tabbata akwai network service mai kyau.
  3. Da zarar ya buɗe babu abinda ya rage sai printing.

Hukumar ta sawwaƙa yadda za’a duba sakamakon, wanda yake da salula hannu ma zai iya dubawa, sannan kuma za’a iya garzaya izuwa internet café mafi kusa domin dubawa a ko ina.

Muna fatan dukkan ɗalibai zasu karɓi sakamakon nasu cikin nishaɗi gami da murmusawa!

Dannan wannan rubutu domin duba sakamakon jarrabawar: https://www.stsbkano.ng/

Share:

administrator