Hausa

Mun shirya tsaf domin kawar da talauci a tsakanin ‘yan Najeriya – Minista Sadiya

Ministar Agaji da Jinkai da Bala’i da Ci gaban Jama’a Hajiya Sadiya Umar Farouq ta jaddada aniyar gwamnatin tarayya na ganin an kawar da talauci a tsakanin ‘yan Najeriya ta hanyar shirye-shirye da tsare-tsare daban-daban da gwamnatin Buhari ta bullo da su.

Ministar ta bayyana hakan ne a wajen taron kaddamar da tallafin ga marasa galihu da aka gudanar a Kano, Talata.

Ministan wanda babban sakatare a ma’aikatar, Dr. Nasiru Sani Gwarzo ya wakilta, ya ce tun kafuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015 ta gaji matsalar talauci da ya kai kashi 70 cikin 100.

Ta ce gwamnatin tarayya ta kara maida hankali wajen samar da hanyoyin magance matsalolin da ke addabar talakawa da marasa galihu kasar nan duk da wasu kalubalen tattalin arziki da gwamnatin ta gada a lokacin.

“Tun lokacin da aka fara aiwatar da tsarin NSIP a shekarar 2016, ya yi tasiri mai kyau ga yawancin rayukan talakawa da marasa galihu a Najeriya.

“Ni da kaina na ga irin abubuwan da suka canza rayuwa na mutanen da, a halin yanzu, suna rayuwa ƙasa da layin fatara da waɗanda ke fuskantar bala’i amma yanzu suna rayuwa mafi kyau.

“A yau, mun zo ne domin kaddamar da shirin bayar da tallafi ga kungiyoyi masu rauni (GVG) a jihar Kano, aikin da aka bullo da shi a shekarar 2020, wanda aka fara a matsayin Grant for Women Rural (GRW), don dorewar ajandar hada kan al’umma na Gwamnatin Shugaba Buhari. . Ya yi dai-dai da shirinsa na kasa na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10,” inji ta.

Ministan ya bayyana cewa, GVG an tsara shi ne domin bayar da tallafin kudi na naira 20,000.00 a lokaci daya ga wasu daga cikin matalautan Najeriya masu fama da talauci a yankunan karkara da yankunan birane a fadin jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya, don karfafa wa masu cin gajiyar damar inganta ayyukansu na kasuwanci, musamman da nufin fitar da su daga kangin talauci.

A nasa jawabin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Usman Alhaji, ya yaba da irin hangen nesa da jajircewar gwamnatin tarayya wajen bullo da tsare-tsaren da suka shafi magance matsalar talauci a kasar nan.

Related Articles

Back to top button